Austriya ta tsawatarwa Girka kan 'yan gudun hijira
March 3, 2016Talla
Ministan ya ce akwai bukatar mahukuntan Girkan dakatawa da yiwa sabbin masu neman mafakar rijista a sansanonin da aka kebe.
Sebastian Kurz a yayin da yake zantawa da mujallar Sueddeutsche Zeitung ta Jamus yayi nuni da cewar akwai bukatar kawo karshen munufar Girka wajen haramtawa masu gudun hijirar tsallakowa turai, a inda ya kara da cewar wadanda suka samu suka tsallako zuwa Girka a iya barin su.
Yanzu haka dai mashiga biyu ce 'yan gudun hijirar ke amfani dasu wajen tsallakowa da suka hada da kasashen Girka da Italiya domin bazamowa cikin kasashen turai, a inda kasashen ke cigaba da samun suka daga takwarorin su na turai kan rashin tabuga komai wajen dakile kwararar 'yan gudun hijiran zuwa turan.