1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Azabtar da fursunoni a gidan yarin Makala

July 25, 2024

Wani dan jarida a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ya bankado yadda fursunoni ke shan bakar wahala a babban gidan yarin Makala da ke Kinshasa babban birnin kasar

https://p.dw.com/p/4iio2
Gidan yarin Kinshasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar  Kongo
Gidan yarin Kinshasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KongoHoto: ALEXIS HUGUET/AFP

Stanis Bujakera ya shafe kusan wata bakwai a matsayin fursuna a gidan yarin sannan daga bisani ya shaki iskar 'yanci tare da aniyar nuna wa duniya halin da gidan mazan na Makala ke ciki.

Wasu daga cikin hotunan da dan jarida Stanis Bujakera ya dauka sun nuna yadda fursunoni ke layi suna karbar jan tuwo da kuma miyar ganye da babu alamar gata a cikinta.

Idan aka dubi batun kiwon lafiya kuma lamarin ya kazanta saboda a kasa zaka ga fursunoni na kwance da raunuka a jikinsu, wasu suna fama da rashin lafiya amma babu kulawa a haka da yawa ke mutuwa a cewar dan jaridar.

Makala kamar jahannama take. Makala wuri ne da mutum biyu ko uku ke mutuwa a ko wace rana. Kwana biyu da suka gabata, na ga mutum har shida sun mutu a rana guda. Cunkoso da rashin iskar shaka na kashe mutane. Wasu kuma rashin lafiya akwai mutane da ke da cututtuka daban-daban na kalli mutane da dama wadanda basu iya ko tafiya"

Shima dai dan jarida Stanis Bujakera da ya kasance daya daga cikin masu gidan jaridar "Actualite.cd." ya shafe kusan wata bakwai ya na zaman jiran shari'a a gidan yarin na Makala kafin ya shaki iskar 'yanci a watan Afrilun da ya gabata.

Tun a lokacin mulkin mallaka a shekarar 1957 ne aka gina gidan yarin na Makala wanda aka tsara zai dauki fursunoni 1,500, amma a yanzu akwai mutum 15,000.

Akasarinsu ba a yanke musu hukunci ba kuma suna garkame a can. Dan jaridar dai ya ce ya ga abin al'ajabi.

Na hadu da wani fursuna a lokacin da nake can. Tun a shekarar 2018 ake shari'arsa sannan aka yanke mishi hukunci a shekarar to amma ba shi da masaniya a kan yadda zai bibiyi shari'ar a haka ya rika zama a gidan yarin har 2023 ma'ana kenan ya bar gidan yarin shekara biyar bayan an yanke masa hukunci."

Wadannan hotuna da bidiyo da aka dauka sun nuna irin ukuba da fursunoni ke sha a gidan yarin na Makala dake birnin Kinshasa na Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo

Rayuwarsu ta kasance tamkar a wata duniya ta daban gashi sau daya suke cin abinci a rana kuma shi dinma mara inganci.

Sai dai a martaninta ga wannan binciken na dan jaridar, gwamnatin Kongo ta ce bidiyon da ya dauka tsoho ne na shekaru-aru amma yanzu lamarin ba haka yake ba.

 Ministan shari'a na Kongo Constant Mutamba ya yi ikirarin cewa gwamnati na kokarin ganin ta rage cinkoso a duk gidajen yarin kasar

Ya kuma kara da cewa gwamnati na samarwa fursunoni abinci da magunguna isassu kuma lamarin bai kazanta kamar yadda ake tsammani ba.