Azerbaijan ta yi watsi da taro da Armenia
October 4, 2023An gayyaci Aliyev domin halartar tattaunawar ta bangarori biyar da kungiyyar tarayyar Turai ta shiga tsakani wanda aka tsara za a yi a Granada, kasar Spain.
An shirya shugabannin kasashen Jamus da Faransa da kuma shugaban majalisar tarayyar Turai Charles MIchel za su halarci taron.
Tattaunawar za ta mayar da hankali ne akan makomar yankin Nagorno-Karabach, tsohon yankin yan kabilar Armenia da ke cikin Azerbaijan, yankin da Azerbaijan ta kwace a artabun da suka yi a ranar 19 ga watan Satumba wanda ya jawo gagarumin kaurar jama'a da kuma zargin kokarin kakkabe yan kabilar Armenia daga doron kasa.
Firaministan Armeniya Pashinyan ya ce duk da haka ya kudiri aniyar zuwa Spain domin halartar taron kolin na kungiyar tarayyar Turai, yana mai cewa abin kunya ne janyewar da Aliyev ya yi na kin halartar taron.