1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba alamar sasanta rikicin Gabon

Usman Shehu UsmanSeptember 8, 2016

An dage shirin zuwan tawagar kungiyar Tarayyar Afirka don shiga tsakani a rikicin kasar ta Gabon har sai illa masha Allahu.

https://p.dw.com/p/1JygQ
Ali Bongo Ondimba Gabun
Hoto: picture-alliance/dpa/D.Honl

Wata sanarwar da ministan harkokin wajen kasar ta Gabon Emmanuel Issoze Ngondet ya bayar, ta bayyana cewa tawagar kungiyar Tarayyar Afirka, da aka tsara za ta ziyarci Gabon daga wannan Juma'ar, a yanzu an soke tafiyar kuma ba wata sabuwar rana da aka tsayar na zuwan tawagar. A cewar ministan harkokin wajen kasar ta Gabon, shugaban kasar Chadi Idriss Deby wanda ya kamata ya jagoranci tawagar zuwa Libreville, ba zai samu zuwa ba domin ya dawo daga taron kungiyar G20 da ya gudana a kasar China, kuma yana cike da gajiya, a fadar mahukuntan na Gabon. Kawo yanzu dai babu martanin da aka samu daga kasar Chadi, duk kuwa da cewar duniya ta zuba ido ga tawagar ta kasashen Afirkan, domin ganin ko za ta warware rikicin siyasa da ya barke bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.