Ba a cimma tudun dafawa ba a taron kasar Siriya
April 27, 2016Talla
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Siriya Staffan de Mistura ya yi wata ganawa ta karshe a daidai lokacin da ake dab da kammala zagayen tattauna batun neman zaman lafiyar kasar Siriya ba tare da wani cigaba na a zo a gani ba. A daren wannan Larabar za a kawo karshen tattaunawar a birnin Geneva. De Mistura ya bayyana ranar ta yau da wata muhimmiyar rana, sai dai ba bu alamun cimma tudun dafawa a tattaunawar zagaye na uku da aka fara a ranar 13 ga watan Afrilu da nufin kawo karshen yakin basasar Siriya na tsawon shekaru biyar. Ko da yake babbar kungiyar adawar Siriya ta janye daga zauren taron amma an ci gaba da tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin Siriya da wasu kungiyoyi biyu na 'yan adawa.