1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babbar haduwar farko ta Trump da Putin a Helsinki

Salissou Boukari
July 16, 2018

A wannan Litinin ce ake babbar haduwa ta farko tsakanin Shugaban Amirka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a birnin Helsinki na kasar Finlande.

https://p.dw.com/p/31VbY
Treffen Putin und Trump in Helsinki Protest
Hoto: DW/T. Schultz

Wannan babban zaman taro tsakanin shugabannin manyan kasashen biyu na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka ta tabarbare tsakaninsu sakamakon zarge-zargen da Amirkan ke yi wa kasar ta Rasha musamman ma kan batun kutse a lokacin zaben shugaban kasar ta Amirka. Baya ma ga wannan batu, akwai kuma batutuwa irin su rikicin gabashin Ukraine, da Siriya da ma Iran da ake ganin za su mamaye wannan zaman taro na tsakanin shugabannin manyan kasashen biyu.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha da ake yi wa kallon shugaba mai karfi, da kuma Donald Trump na Amirka da ake yi wa kallon mai cike da basira, sun sha kyalla wa juna idanu tare da nuna damarsu ta inganta huldar da ta yi tsami a tsakanin kasashen biyu. Sai dai kuma a baya kasar ta Amirka ta yi karin takunkumi ga Rasha, tare da korar jami'an diflomasiyyar kasar ta Rasha da dama daga Amirka, matakin da Rashan ta mayar da martani a kan shi.