Jamus ta sa sabbin dokokin corona
December 2, 2021Talla
Dokar da tuni ta fara aiki a wasu jihohin kasar, za a fadada ta zuwa ko ina ba tare da la'akari da yanayin girmar cutar ba, cikin sabbon dokokin da gwamnatin ta amince a wannan Alhamis, har da rufe gidajen rawa idan aka tabbatar da karuwar masu kamuwa da cutar a cewar Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Yanzu haka dai majalisar dokokin Jamus na duba yuwar tilasta allurar rigakafin corona kan kowa da kowa daga watan Febrairu na shekarar 2022.