1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba wani shirin daukar matakin soji kan Iran a yanzu

September 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bukr

Bayan cikar wa´adin da MDD ta bawa Iran na ta dakatar da shirin ta na nukiliya da ake takaddama a kai, ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya ce babu wani shiri na daukar matakan soji kan Iran. A cikin wata hira da tashar telebijin ta Jamus mista Steinmeier ya ce babu kasa daya daga cikin kasashe 6 da suka zauna kan teburin shawarwari a cikin watannin da suka wuce, da ta tabo batun yin amfani da karfin soji. A cikin wani rahoto da ta gabatarwa kwamitin sulhun MDD a jiya hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA ta ce Iran ba ta amsa kiran da aka yi mata na ta daina sarrafa sinadarin uranium ba. A halin da ake ciki Iran ta yi watsi da wannan rahoto tana mai cewa ba zata saduda da matsin lamba daga ketare ba, domin shirin ta na nukiliya na lumana ne. Amirka na matsawa da a kakaba mata takunkumi, yayin da China da Rasha ke taka tsatsan wajen daukar wannan mataki.