1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba´a cimma tudun dafawa ba a taron tantance makomar Kosovo

March 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuQ0

Wakilin MDD na musamman Martti Ahtisaari ya ce an tashi baram-baram a tattaunawar da ake yi tsakanin shugabannin Sabiya da Albaniyawan Kosovo akan wani shirin MDD dangane da makomar lardin Kosovo da ake takaddama a kai. Shirin wanda aka gabatar a cikin watan fabrairu ya tanadi warware takaddamar da ake yi bayan rushewar tarayyar Yugoslabiya a cikin shekarun 1990. Ko da yake shugabannin kabilar Albaniyawa sun amince da shirin amma jami´an Saqbiya sun yi watsi da shi. Taron na birnin Vienna ya kawo karshen tattaunawar da aka shafe watanni 14 ana yi tsakanin sassan biyu. Wakilin MDD Martti Ahtisaari ya ce zai aike da shirin wanda ya tanadi share fagen bawa Kosovo ´yanci ga kwamitin sulhuin MDD a karashen wannan wata.