1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban Taron FDP a Dresden

June 7, 2004

Jam'iyyar FDP ta kammala babban taronta a Dresden tare da kiran shiga yakin neman zabe tattare da kwarin guiwa, saboda zaben da za a gudanar a shekara ta 2006 ka iya kasancewa wata dama ta karshe a gare ta a fafutukar sake shiga a rika damawa da ita a al'amuran mulki

https://p.dw.com/p/Bvj5
Shugaban jam'iyyar FDP Guido Westerwelle, lokacin taron jam'iyyar a Dresden
Shugaban jam'iyyar FDP Guido Westerwelle, lokacin taron jam'iyyar a DresdenHoto: AP

A lokacin da yake jawabi a zauren taron, shugaban jam’iyyar FDP Westerwelle yayi nuni da abin da ya kira wai wata dama ta biyu, inda yake nufin zaben majalisar dokoki ta Bundestag da za a gudanar a shekara ta 2006. Fatansa game da haka shi ne ganin jam’iyyarsa ta sake komawa ana damawa da ita a al’amuran mulki kafin wannan lokaci ta yadda zata warkar da radadin tabon kayen da ta sha a zaben shekara ta 2002. Wannan ba kawai wata dama ce ta biyu ga jam’iyyar ba, kazalika har da shi kansa shugabanta. Domin kuwa da yawa daga ‚ya’yan jam’iyyar mai sassaucin manufofin siyasa na tattare da ra’ayin cewar Westerwelle, shi ne ummal’aba’isin bakin jini da take da shi tsakanin jama’a, saboda bai ankara da illar da marigayi Jürgen Möllemann yayi wa jam’iyyar akan lokaci ba sai bayan da bakin alkalami ya riga ya bushe. FDP ta dade tana fama da radadin wannan illa kuma har yau tana ci gaba da yarfe gumi a kokarin dawo da martabarta tsakanin jama’a ta yadda za a sake rungumarta da hannu biyu-biyu. A dai halin da muke ciki yanzun jam’iyyar ta FDP na bin wata zazzafar akida ce ta canjin manufofin tattalin arziki da jin dadin rayuwar jama’a, abin da ya hada har da kirkiro wasu bangarori na musamman da zasu taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin yankin gabacin Jamus da kuma mayar da harkar inshorar kiwon lafiya kacokam ga kamfanoni masu zaman kansu. Kazalika da so samu ne da jam’iyyar FDP zata fi kaunar ganin an ba wa nahiyar Turai baki dayanta wata kujera ta dindindin a kwamitin sulhu na MDD a maimakon Jamus ko kuma daidaikun kasashen na Turai a wawware.

Babu dai wani sabanin da aka fuskanta a siyasance a lokacin babban taron na dresden. A maimakon haka an samu gagarumin hadin kai domin magana da murya daya a tsakanin illahirin mahalarta taron su kimanin wakilai 662. Mutumin da ya taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan ci gaba kuwa shi ne tsofon shugabanta kuma kakakin wakilanta a majalisar dokoki Wolfgang Gerhardt, wanda a cikin jawabinsa yayi kira ga wakilan da su nuna kwarin guiwa domin dogaro da kansu su kuma kutsa yakin neman zabe a cikin gadin gaba. Nan da karshen wannan makon dai za a ga makomar wannan hadin kai da wakilan jam’iyyar ta FDP suka nunar. Idan har jam’iyyar ta tsallake kashi biyar cikin dari da take bukata a zaben majalisar Turai da kuma zaben jihar Thüringiya ranar lahadi mai zuwa, hakan zai bayyana muhimmancin da take da shi domin taka rawar gani a siyasar kasa baki daya. Amma in har ta sha kaye kuwa to ba shakka FDP zata samu kanta a cikin wani mawuyacin hali na kaka-nika-yi. A saboda haka ya zama wajibi jam’iyyar tayi amfani da wannan dama ta biyu ta shugabanta ke batu akai, saboda in har wannan dama ta kubce mata to da wuya ta samu wata ta uku.