Babban taron MDD karo na 77
September 20, 2022Talla
A gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara karo na 77 da ke budewa a wannan Talatar a birnin New York, ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta jadadda mahimmancin rawar da MDD ke takawa wajen shawo kan rikice-rikice a duniya.
Baerbock ta kuma ce, taron na bana zai sha bam-bam da wadanda suka gabata yayin da take kalubalantar Rasha kan watsi da ka'idojin da aka kafa Majalisar da kuma mamayar da ta yiwa Ukraine.
Ana dai ganin mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine shi ne zai mamaye tattaunawar a taron na bana. Fiye da shugabanin duniya 140 ne ake sa ran su halarci taron na tsawon mako guda da zai gudana a birnin New York na kasar Amirka.