120510 Kirchentag Afrika
May 13, 2010A birnin Munich na nan Jamus daga wannan Laraba zuwa ranar Lahadi ake gudanar da babban taron ƙungiyoyin coci-coci mai taken "Domin ba ku kyakkyawan fata". Taken taron dai na da muhimmanci musamman ga mazauna yankuna da ake fama da rigingimu kamar a Sudan, Chadi da janhuriyar Afirka Ta Tsakiya. A dukkan ƙasashen uku shugabanninsu sun ɗare kan kujerar mulki ne sakamakon juyin mulki, sannan dukkan ƙasashen uku na fama da mummunan tasirin rikicin Darfur. Ƙungiyoyin addini ƙalilan ne ke iya yin wani aiki na a zo a gani a cikin wannan mawuyacin yanayi.
Fada Paolino Tipo Deng daga ƙasar Chadi har yanzu yana tunawa da ranar da 'yan tawaye suka kutsa cikin birnin N'Djamena kimanin shekaru biyu da suka gabata, suna neman farma fadar shugaban ƙasa amma a ƙarshe aka fatattake su. Abin da ya faru a wannan rana ya ƙara sa Fada Tipo Deng gane muhimmancin ayyukan ƙungiyoyin addini a Chadi. Yana shugabantar wata cibiyar tuntuɓar juna tsakanin Kiristoci da Musulmai a babban birnin ƙasar ta Chadi.
"A dole muna faɗa a fili idan 'yan siyasa suna abubuwan da bai kamata su yi ba. Muna tir da yaƙin, muna kira ga gwamnati da kuma 'yan tawaye da su tattaunawa da juna kan neman hanyar zaman lafiya domin a yi sulhu."
Fada Tipo Deng na nuna takaicinsa yadda ake ɓatar da dubban miliyoyin kuɗaɗen shiga daga arzikin man fetir maimakon amfani da su ga al'ummar ƙasa. Shugaba Idris Deby wanda tun shekaru 20 da suka wuce ya hau kan karagar mulki yana amfani da kuɗaɗen da aka warewa don yaƙi da talauci, yana sayen makamai domin ƙarfafa ikonsa. A matsayinsa na wakilin coci, Fada Tipo Deng na iya bayyana ra'ayinsa saɓanin sauran al'ummomin ƙasar. To sai dai yana takatsantsan wajen sukar gwamnati, maimakon haka ya fi mayar da hankali kan aikinsa na taimakawa 'yan gudun hijira, musamman daga lardin Darfur waɗanda ke kwarara zuwa Chadi domin samun wata kyakkyawar rayuwa.
Rikicin Darfur ya tilastawa mutane kimanin miliyan uku bazuwa a yankin baki ɗaya inda suke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a ƙasashe maƙwabta kamar Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya, inda ƙungiyoyin addini ke taimaka musu. Ɗaukacin al'ummar Afirka ta Tsakiya Kiristoci ne yayin da 'yan gudun hijirar kuma Musulmai ne, inji Boris Modeste Yakoubou malamin Falsafa a jami'ar birnin Bangui kuma yanzu haka yake faɗakarwa game da nuna juriya ta addini.
"Da farko da wuya domin masu matsanancin ra'ayi na masu ganin cewa wannan haɗin kan ba zai yiwu ba. Amma sannu a hankali mun samu nasarar fahimtar da su cewa nuna bambamci bai da ma'ana. Yanzu haka dai muna samun kusanta da fahimta da kuma nunawa juna zumunci."
Ga Boris Yakoubou wannan kusanci na addini shi ne sharaɗin farko na samun kwanciyar hankalin siyasa. A saboda haka ba kawai gwamnati ba, a'a yana kuma shigar da ƙungiyoyin farar hula a cikin aikinsa.
"Har yanzu matasa na nuna taurin kai. Ba sa nuna sha'awa saboda suna da wata damuwa daban. Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya ta yi fama da matsalolin siyasa da na tattalin arziki, su kuma matasan suna sanya dogon buri daga shugabanni. Saboda haka ba su damu da ayyukanmu ba."
Ayyukan ƙungiyoyin addinin dai suna jawo hankali matasan cewa su ma za su iya taka rawa wajen kawad da mulkin kama karya.
Mawallafa: Adrian Kriesch / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi