MDD: Amincewa da yankin Falasdinu bisa manufa
May 10, 2024Talla
Kasashe mambobin Majalisar 143 ne suka kada kuri'ar amince wa da kara daukaka darajar Falasdinu yayin da wasu tara suka kada kuri'ar kin amincewa baya ga wasu 25 da suka kaurace wa kada kuri'a. Kudurin ya kara bayar da dama ga karin rawar da Falasdinawa za su taka a zauren, tare da yin kira ga kwamittin sulhu na Majalisar ya amince da Falasdinun ta zama cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya.
Karin bayani: Falasdinu na son dauketa a matsayin kasa
Yayin da take mayar da martani, ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ta ce, kuri'ar da zauren ya kada ya nuna cewa sun cacanci zama cikakkun mamba.