Laifukan take hakkin dan Adam na ci gaba da kazanta
December 10, 2018Duk da cewar bai wajaba a kan kasashe na amincewa da kudurin kare hakkin dan adam din ba, a hukumance babu kasar da ta fito fili ta nuna rashin muhimmancinta. A cewar tsohon kwamishanan hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya Seid Read al-Hussein, albarkacin wannan kuduri mutane da dama a sassa na duniya na da 'yancin walwala da kulawa ta musamman, godiya ga sashi na 217 na kudurin kare hakkin dan Adam da aka cimma a ranar 10 ga watan Nuwamban shekara ta 1948 a birnin Paris din kasar Fsaransa.
Miliyoyi na rayuwa a yanayi na bautar zamani
Ko Majalisar Dinkin Duniya ta yi amanar cewar wannan kuduri na ji da jiki, wajen rashin kulawa da shi. Alal misali bautar da mutane a zamanance da azabtarwa ko kuma abin da za'a kira take hakkin gudun hijira, na daga cikin manyan hanyoyin watsi da wannan kuduri. A cewar wata gidauniya mai fafutukar kare 'yancin mutanen da ake bautarwa, mai suna Australian Walk Free Foundation dai, sama da mutane miliyan arba'ain ke rayuwa cikin yanayi na bautar zamani a wannan karni da muke ciki.
A yanzu haka dai Koriya ta Arewa da Iritriya da Burundi da Jamus da kuma Birtaniya na daga cikin kasashen da za'a iya cewar abun da ake yi don tsayar da wannan dabi'a bai taka kara ya karya ba. Hakan na aukuwa ne ta hanyar matan da ake tilastawa karuwanci da wadanda ake ci da guminsu, daura da sayen kayayyakin da mutanen da ake bautarwa suka sarrafa.
Majalisar Dinkin Duniya ta kalubalanci matakin azabtarwa
Kudurin kare hakkin bil adaman kazalika ya sanya wasu nau'oi na hukunci kamar amfani da wayoyin lantarki, ko kebe mutum da ma cin zarafi a matsayin wasu nauo'i na azabatarwa, wadanda ake samu a wasu kasashe na duniya kamar Turkiyya da Masar. Kwararru na bayyana fargaba dangane da halin da 'yan gudun hijira suka tsinci kansu a ciki, misali a Amurka. A daya bangaren kuma an yabawa kasashe irinsu Yuganda da Ruwanda da Habasha Hondorus kan yadda suka marabci 'yan gudun hijira, halin da ya dace sauran kasashen duniya su yi koyi da shi.