Jaridun Jamus: Babu zabe a Mali
January 14, 2022A cewar ECOWAS ta dauki wannan matakin ne bayan wanin taron da suka gudanar a Accra babban birnin kasar Ghana, a taron da kuma ya samu halartar wakilin ECOWAS a sasanta ricin mali kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da kuma shugaban kungiyar ta ECOWAS, Jean-Claude Brou. Bayan daukar matakin, ECOWAS ta kuma bukaci kasashen kungiyar AU da Trayyar Turai da Majalisar Dinkin duniya su bi sahun matakin da ECOWAs ta dauka.
Ita ma jaridar Berliner Zeitung ta duba kasar ta Mali amma kan batun sojojin kiyaye zaman lafiya a Mali. Shugabar kwamitin kula da tsaro ta majalisar dokokin Jamus Marie-Agnes Strack-Zimmermann, tace ana daukar matakan gaggawa na kare rundunar sojojin Jamus da ke kasar Mali. A gefe guda kuma ta bukaci da kada a yi gaggawa, wajen fitar da sojojin Jamus daga kasar ta Mali, shugabar kwamitin tsaron ta kuma soki yadda gwamnatin sojan Mali ta kulla hulda da sojojin kasar Rasha. Don haka ta yi gargadi kan duk wani shirin janye dakarun kasar daga Mali.
Yara sun koma makaranta a fadin kasar Yuganda. Jaridar die tageszeitung ta rubuta wannan labarin. Jaridar ta ce bayan makwanni 83 daga karshe yara yan makaranta sun koma karatu, abinda ya zame wa kasar tamkar wani biki. Yaran kasar Yuganda an hana su zuwa makaranta ne tun bullar annobar corona a duniya, inda a lissafi yanzu kimanin shekaru biyu babu makarantu a kasar, abinda ya sa Yuganda ta kasance kasa mafi dadewa makarantunta na rufe bisa annobar corona a duniya baki daya. Yara dai sun yi ta tsalle da murnar ganin an dawo wa makaranta.
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung, ta duba gasar cin kofin kwallon kafan Afirka ne da aka bude a kasar Kamaru. Jaridar tace alkalin wasa ya busa sau biyu tun gabanin lokaci. Lamarin ya faru ne a wasa tsakanin Mali da Tunisiya, inda alkalin wasa mai shekaru 42 dan kasar Zambiya, ya hura a tashi wasa tun miniti hudu gabanin cikar lokaci wato anan minti 86. Bayan da kasar Tuniyasa ta nuna bacin ranta alkalin wasan ya nemi gafara kuma ya sake cewa a ci gaba da wasan da lokacin Mali na da ci daya Tunisiya na nema.