Badakalar leken asiri a Jamus
May 7, 2015
Bayan harin ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2001, inda dubban mutane suka rasa rayukansu, yaki da ta'addanci ya dauki sabon salo a fadin duniya. Kasashe sun karfafa dokokinsu, kuma Jami'an leken asirin kasashen Yamma sun kaddamar da ayyukan hadin kai a tsakaninsu, sai dai a halin da ake ciki, kasashen Yamman sun fara zargin juna da satar bayanai, abin da ke janyo cece-kuce tsakanin 'yan siyasa, musamman nan Jamus da Turai baki daya.
Irin wannan hadakar ce ma ta hada hukumar leken asirin Amirka na NSA da kuma na Jamus BND, sai dai bisa dukkan alamu ba su yi la'akari da dokokin da ke tattare da yin hakan ba, kamar yadda suka bayyana a bayanan da kwararre kan komputan nan, Edward Snowden ya wallafa, tare da tallafin wasu jaridu na kasa da kasa.
A ciki ne Snowden mai samun mafakar siyasa a Rasha, ya gano cewa cikin tsawon shekaru biyu, yanzu hukumar ta NSA tare da hukumar kula da sadarwar Birtaniya na sauraron duk wata sadarwa da aka yi ta wayar tarho a kasashen duniya. Kuma ta hanyar yin haka, ba tattaunawar masu kulla ta'addanci kadai ake sauraro ba, bisa bayanan kafofin yada labarai, har ma da tattaunawar gwamnatoci, da kamfanoni na tattalin arzikin kasashe kawaye.
Daga cikin wadanda aka saurara har da kamfanin da ke kera jirgin sama na AIRBUS da kuma majalisar dokokin Turai. Mahimmancin wannan da ma irin sauran matakan da aka dauka ga yaki da ta'addancin ne ke ci-gaba da daukar hankali tsakanin 'yan siyasan Jamus da sauran kungiyoyin siyasar Turai.
Tsawon shekara guda yanzu, majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, ke gudanar da wani bincike dangane da hukumar NSA, inda ta riga ta yi wa mambobin hukumar leken asirinta na BND, kuma har wa yau za ta sake yi wa wasu. A wannan bincike ana zargin ma'akatan hukmar ta BND ne da baiwa hukumar leken asirin Amirka bayanai, na al'ummomin Jamus da wasu kasashen Turai, ba bisa ka'ida ba. Daga cikin shaidun da za a yi wa tambayoyi, har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wadda aka saurari bayanai daga wayar tarhon ta a shekara ta 2013. A lokacin da aka gano wannan ta'asa, ga irin martanin da Merkel ta mayar.
"Har yanzu tambaya ta ita ce, dan me wata kasa za ta rika leken asirin kawayenta? musamman ma abubuwan da ke da mahimmanci sosai. A tunani na, amsar ita ce, bai kamata ma a ce hakan ya faru ba"
To sai dai ga wadanda ke kalubalantar gwamnatinta, suka ce Merkel, ba ta taka wata rawar gani ba, wajen fayyace badakalar sauraran bayanan da ya afku tsakanin kasashen. Jam'iyyun adawa irinsu Die Linke masu ra'ayin sauyi, da kuma The Greens masu rajin kare muhalli, suna zarginta da yin sakacin da ya kai ga majalisar dokokin Amirka ta sami bayanai masu mahimmancin gaske. A wata hira da wata tasha mai suna Radio Bremen ta yi da Angela Merkel, ta kare hadin kan da ke tsakanin hukumomin leken asirin Jamus da Amirkan, da cewa a cikin yanayin tsaron da duniya ta ke yanzu, kasar na bukatar irin wannan hadakar, ta kuma kare matakin da ta dauka
Ta ce: "Zan ba da amsa, a can wurin da ake bukata, wurin da ake gudanar da bincike idan har aka tambaye ni. A wurin ne zan bayyana duk abin da ake son sani"
Yanzu haka dai wannan batun ya dauki hankalin siyasa da kuma kafafen yada labaran kasar ta Jamus baki daya.