Badakalar siyasar kasar Masar
February 6, 2014Wannan aniya ta Field Mashal Abdel Fattah al-Sisi, da aka dade ana jiran bayyanar ta a fili dai, ka iya kara rura wutar tashe-tashen hankulan da Masar din ke fama da su tun bayan da Al-Sisin ya jagoranci sojoji suka kifar da gwamnatin hambararren tsohon shugaban kasar Muhammed Morsi a shekarar da ta gabata.
Wata jaridar kasar Kuwaiti ta ruwaito Al-Sisi na cewa ba zai ki amincewa da kiraye-kirayen tsayawa takara da al'ummar kasar Masar din ke yi masa ba, a dangane da hakan zai tsaya takarar shugabancin kasar a zabukan da za a gudanar a nan gaba. Masana dai na bayyana wanannan aniya ta Al-Sisi da cewa Masar din za ta sake komawa kan tafarkiun mulkin soja bayan gagarumin juyin-juya halin da ya afku a kasar a shekara ta 2011 da ya yi awon gaba da kujerar mulkin tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu