1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annalena Baerbock na ziyara a China

Abdourahamane Hassane
April 14, 2023

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock na ci gaba da yin ziyarar aiki a China.

https://p.dw.com/p/4Q54T
Annalena Baerbock tare da ministan harkokin wajen China Han Zheng
Annalena Baerbock tare da ministan harkokin wajen China Han ZhengHoto: Kira Hofmann/photothek/IMAGO

Ministan na yin ziyarar ne da nufin ganin Chinar ta yi wani yunkuri kan Rasha domin shawo kanta ta kawo karshen yakin Ukraine. Saboda ta ce babu wata kasa da ke da tasiri kan Rasha kamar China: ''Ina tambayar kaina mai ya sa har yanzu Chinar ta gaza yi wa Rasha magana ta tsaida yaki, ganin cewar Putin na sauraran China,mu dukkaninmu mun san cewa shugaban Rashan zai amince da shawarar Chinar. Minista ta ci gaba da cewar suna son kamar yadda kasar China ta samu nasarar shiga tsakanin Iran da Saudiyya, ta matsa wa Rasha lamba domin a daidaita: