Ministar Jamus tana ziyara a Afirka
July 15, 2024Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock a wannan Litinin tana fara ziyarar zuwa wasu kasashen yankin yammacin Afirka da suka hada da Senegal da Cote d'Ivoire da nufin karfafa hulda gami da kare ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Sahel na Afirka.
Karin Haske: Ministar harkokin wajen Jamus za ta kai ziyara yammacin Afirka
Gabanin fara ziyarra ministar ta ce karin samun kasashe karkashin rikice-rikice a yankin zai kara tabarbara lamura kuma tana fata nada shugaban kasar Senegal mai shiga tsakanin kasashen Afira ta Yamma da wadanda suka samu sabani haka zai iya kyautata yanayin da ake ciki. Kasashen na Senegal da Cote d'Ivloire inda ministar harkokin wajen ta Jamus, Baerbock za ta kai ziyara suna cikin kasashen da ke karkashin tsarin mulki na farar hula.