Amurka da Houthi na rikici a Bahar Maliya
December 24, 2023Kakakin kungiyar ta Houthi ta Yemen Mohammed Abdul-Salam ya ce jirgin ruwan dakon kayan mallakar kasar Gabon da makami maai linzamin da Amurkan ta harba ya fashe a kusa da shi, na kan hanyarsa ta zuwa Rasha ne. Ya kara da cewa Tekun Bahar Maliya zai zama tungar yaki, in har Amurka da kawayenta suka ci gaba da cin zarafinsu. A cewarsa tilas kasashen da ke makwabtaka da tekun, su fahimci irin barazanar da hakan ke nufi ga tsaron kasashen nasu. Da ma dai shugaban kungiyar ta Houthi Abdel-Malek al-Houthi ya yi gargadin cewa za su kai hari a kan jiragen ruwan yakin Amurka da ke Tekun Bahar Maliyan, in har Washington ta kai musu hari bayan da ta kafa wata runduna ta musamman ta kasa da kasa domin mayar da martani ga hare-haren 'yan Houthi ga jiragen ruwan dakon kaya a Tekun na Bahar Maliya.