Bajinta a wasannin lig na kasashen Turai
May 8, 2023A wasannin Pirimiya na Ingila inda Mohammad Salah ya jefa kwallo na 100 a raga inda ya zama dan wasan Liverpool na farko da ya jefa kwalo a raga a wasanni tara a jere bayan jefa kwallo daya tilo da kungiyar ta samu nasara kan Brentford a karshen mako. Mohammad Salah dan kasar Masar yana cikin wadanda tauraronsu ke haskawa a wasannin na Pirimiya.
Sannan kungiyar Manchester City ta doke Leeds 2 da 1, kana West Ham ta doke Manchester United 1- 0, yayin da Arsenal ta bi Newcastle gida ta doke ta 2 da nema.
Har yanzu Manchester City ke jagoranci teburin Pirimiya da maki 82, a matsayi na biyu akwai Arsenal mai maki 81, yayin da Newcastle mai maki 65 ke mataki na uku, ita kuma Machester United tana matsayi na hudu da maki 63, sai Liverpool a matsayi na biyar da maki 62.
A wasannin lig na Spain Barcelona ta samu galaba kan Osasuna 1 da nema, abin da ya kara mata tazara kan matsayin farko a teburin da Barcelona ke ci gaba da rikewa. Kungiyar Real Sociedad ta samu nasara kan Real Madrid 2 da nema, sannan Sevilla da doke Espanyol 3 da 2.
Ita dai Barcelona mai rike da teburin La Liga na Spain tana da maki 82, yayin Atletico Madrid take matsayi na biyu da maki 69, kana Real Madrid tana mataki na uku da maki 68.
A wasannin lig na Bundesliga na Jamus Bayern Munich ta bi Werder Bremen har gida ta lallasata 2 da 1, kana schalke ta yi irin wannan tattakin inda ta doke Mainz a gida 3 da 2, yayin da Mönchengladbach ta samu galaba kan Bochum 2 da nema, haka Hoffenheim ta doke Frankfurt 3 da 1. Sannan FC Kolon ta bi Leverkusen gida ta doke ta 2 da 1.
Ranar 20 ga watan Yuli za a kaddamar da gasar cin kofin duniya na kwallon kafa na mata a kasashen Australiya da New Zealand. Ana sa ran za'a sami halartar jama'a a gasar ta FIFA daga kasashen duniya da dama kuma masu sharhi kan kwallon kafa sun ce babu shakka wannan ne karon farko da za'a ga yadda kwallon kafar mata ta habaka kuma ta ke ci gaba da samun karbuwa a kasashen duniya.
Akwai yiwuwar Carlos Alcaraz zai koma matsayi na farko na gwanayen wasan Tennis na duniya bayan nasarar da ya samu a birnin Madrid na kasar Spain kuma yake shirin shiga gasar ta mako mai zuwa a kasar Italiya, zai karbe kambu daga hannun Novak Djokovic.
Firaminista Li Qiang na kasar Chaina ya bayyana adawa da duk wani yunkuri na jefa siyasa a harkokin wasanni sakamakon matsin lamba na dakatar da Rasha daga cikin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya saboda matakin mahukuntan Rasha na kutse kan kasar Ukraine. Shi dai firaministan Chaina ya fadi haka a karshen mako lokacin da yake ganawa da Thomas Bach shugaban hukumar kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya a birnin Beijing fadar gwamnatin Chaina.