1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bakin haure 25 sun halaka sakamakon kifewar kwale-kwale

July 24, 2024

Hukumar kaura ta duniya ta sanar da aukuwar sabon ibtila'i a Tekun Atlantika wanda ya yi ajalin akalla bakin haure 25 yayin da wasu da dama suka yi batan dabo.

https://p.dw.com/p/4ihTH
Überfahrt Mittelmeer Zustände an Bord der Schiffe Überfüllung Flash-Galerie
Hoto: picture-alliance/dpa

Akalla mutane 15 sun halaka sannan wasu sama da 190 sun yi batan dabo bayan da wani kwale-kwale shake da bakin haure ya nutse a gabar Teku a kusa da  Nouakchott babban birnin kasar Mauritaniya kamar yadda hukumar kula da kaura ta duniya ta sanar a wannan Laraba.

Karin bayani: Sama da bakin haure 60 sun sake mutuwa a hadarin jirgin ruwa

Sai dai wani jami'in tsaron gabar Tekun Mauritaniya da ya bukaci a sakaya sunan sa ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sun zakulo gawarwakin akalla mutane 25 sannan kuma sun samu nasarar ceto wadansu mutane 103.

Daga cikin wadanda aka kididdige bayan aukuwar lamarin an samu 'yan Senegal 65 da 'yan Gambiya 52 da kuma dan Cote d'Ivoire guda.

A lokacin take sanar da wannan labari hukumar kula da kaura ta duniya ta nuna takaici kan aukuwar wannan sabon ibtila'i da ke zuwa a daidai lokacin da ake daukar sabbin matakai na dakile kwararar bakin haure zuwa Turai ta barauniyar hanya.