Bala'in ambaliyar ruwa a Pakistan
August 1, 2010Wani jami'in ƙasar Pakistan ya ce yawan mutanen da suka rasu sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da ta afkama yankin arewa maso yammacin ƙasar ya haura mutum dubu ɗaya. Mai kula da ayyukan taimakon gaggawa na Pakistan Adnan Khan ya faɗa a wannan Lahadin cewa yawan waɗanda suka rasu ka iya zarta haka, kasancewar har yanzu akwai wasu wurare a lardin Khyber Pakhtoonkh-Wa da ma'aikatan ceto ba su kai ba tukuna. Hukumomin ƙasar na ƙoƙarin ceto mutane sama da dubu 27 da ambaliyar ruwan ta yiwa ƙawanya a arewa maso yammacin ƙasar biyo bayan kwanaki da dama ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya. To sai dai wani mazaunin ɗaya daga cikin ƙauyukan da ambaliyar ta fi tsanani ya ce mutane kusan miliyan ɗaya ke jiran ɗauki daga gwamnati.
"Ambaliyar ta yi awon gaba da gida na da na maƙwabta na. Wasu maƙwabta na sun mutu, kuma har yanzu akwai mutane ƙarƙashin ɓuraɓusan waɗanda muke ƙoƙarin tonosu. Amma kawo yanzu ba mu ga wani taimako daga gwamnati ko sojoji ba."
To sai dai Janar Athar Abbas dake kula da aikin ceto ya ce suna bakin ƙoƙarinsu na kai taimako a wuraren da ake buƙata.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu