Bala'in gobarar daji a jihar Kaliforniya
Fiye da mutane 75 sun mutu, daruruwa sun bace, dubban gidaje sun kone sakamakon bala'in gobarar daji mafi muni a jihar Kaliforniya ta Amirka.
"Sabon yanayi da ba a saba gani ba"
Gwamnan jihar Kaliforniya, Jerry Brown, ya kwatanta bala'in gobarar dajin ta bana da "Sabon abin da hankali ba ya dauka". A jihar mai fama da fari da kamfar ruwa gobarar daji ce ta haddasa mummunar barna. A arewa wuta ce a wurin shakatawa sannan a kudu wuta ce a yankin Woolsey da kuma Hill, wanda hayakinta ya tirnike sararin samaniyar garin Camarillo, kamar yadda ake gani a wannan hoto.
Dubban mutane suka tsere
Hukumomi a Kaliforniya sun umarci mutane kimanin dubu 150, a yankunan da ke fuskantar barazanar wutar, da su fice. Haka su ma ma'aikata da marasa lafiya a asibitin Feather River a yankin Paradise. Cikin kiftawa da Bisimilla wutar da ke ci daga yankin "Camp Fire" ta mamaye karamin garin da ke arewacin Kaliforniya.
Wuta ta kusan share karaminn garin Paradise
A dole mutane da yawa a Paradise sun gudu sun bar motocinsu saboda wutar. Ala tilas a wata hanya da ke fita daga garin, mutane sun ranta cikin na kare don tsira da rayukansu. Fiye da gidaje 6000 suka kama da wuta. Alkalumman da hukumomi suka bayar sun ce da kyar da gumin goshi aka kashe kusan kashi 25 cikin 100 na wutar a "Camp Fire".
Unguwar attajirai ta Malibu ba ta tsira ba
A yamma da birnin Los Angeles wuta daga yankin Woolsey ta isa unguwar masu hannu da shuni wato Malibu. Gidajen kasaita wato "Villa" da dama ne suka kone kurmus. Shahararriyar mawakiyar Amirka Miley Cyrus da dan wasan kwaikwayo Gerard Butler da mai wasan nishadantarwa Thomas Gottschalk na kasar Jamus, na daga cikin wadanda suka rasa gidajensu.
Asarar rai da yawa
Alkalumman hukuma sun ce mutane 77 suka mutu. An gano gawarwaki a gidaje da kuma a motocin da suka kone. Gobara a "Camp Fire" ta fi janyo yawan asarar rai. Kimanin mutane dubu daya sun bace. Halin dimauta da hanyoyi da aka toshe da rashin hanyoyin sadarwa sun kawo cikas a aikin neman wadanda suka bata.
Rashin sanin yawan barna
Gorar ruwa da ta narke ta malala daga wata mota da ta kone kurmus a Malibu. Barna da asarar da gobarar ta bana ta haddasa a Kaliforniya sun fi na lokutan baya yawa. Ba a taba samun wata gobarar da ta lakume gine-gine masu yawa irin wannan ba. A "Camp Fire" kadai yanki mai murabbba'in kilomita 450, wutar ta lalata.
Aikin kashe gobara mai wahala
Fiye da 'yan kwana-kwana 8000 suka shiga aikin kashe gobarar dajin a Kaliforniya. Daya daga cikin wuraren da gobarar ta fi muni wato "Hill Fire", an kashe kashi 70 cikin 100 sakamakon aiki tukuru na kashe gobara. Hukumomi sun ce za a dauki tsawon makonni biyu kafin a kashe wutar gaba daya, saboda iska da ke kadawa wadda kuma ke kawo cikas ga aikin.
An bar komai ciki
Wata uwa ke nan ke kwantarwa da 'yarta hankali a gaban gidansu da ya kone. Da yawa daga cikin mutane mazauna yankin sun gudu sun bar dukkan kadarorinsu cikin wutar. Ma'aikatan kashe gobara suka umarce mutane da su bar gidajensu don tsira da ransu domin- "gida dai za a iya sake gina shi, amma idan aka yi asarar rai shi ke nan an tafi."