Bam-bamai cikin saƙonni a Girka
November 3, 2010A ƙasar Girka hukumomi sun haramta aika duk wani ƙumshin saƙo izuwa wajen ƙasar har tsawon kwana biyu. An ɗau matakan bayan yan sandan Girka sun gano saƙonni dake ƙumshe da ababen Facewa har 13 a tsakanin shekaran jiya da jiya kaɗai. A jiya wasu saƙonni sun face a ofisoshin jakadancin Rasha da Switziland, yayin da aka samu nasarar warware wasu bama-bamai a ofisoshin jakadancin Bulgeriya da Chile. An kuma kama wani saƙon bam da aka tura ofishin jakadancin Jamus, duk a ƙasar ta Girka. Izuwa yanzu dai jami'an tsaro a ƙasar Jamus suna kan binciken wanda ya aiko wani sako dake ɗauke da bam, izuwa ga shugabar gwamnatin ƙasar Angela Merkel. Wannan ta'addancin dai ana zargin masu tsatsauran ra'ayi na ƙasar ta Girka da shirya shi.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu