1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bam ya tashi a taron 'yan Shi'a a Iraki

Salissou BoukariApril 30, 2016

Fiye da mutane 20 suka mutu wasu kuma kusan 40 suka samu raunuka bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa motar da take cikin a wani jerin gwanon 'yan Shi'a.

https://p.dw.com/p/1Ifl9
Trauernde Frauen nach Bombenanschlag im Irak
Hoto: AP

Wannan hari ya faru ne a Nahrawan yayin da 'yan Shi'a suke kokarin zuwa ziyarar kabarin Musa Al-Kazim wanda yake a matsayin na bakwai daga cikin manyan Limaman Shi'a wanda kuma ya rasu tun a shekara ta 799 Miladiya. A duk shekara dai dubban 'yan Shi'a ne daga kasar ta Iraki da ma Iran suke hallara domin irin wannan ziyara.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafin sada zumunta, kungiyar IS ta dauki alhakin kai wannan hari, inda ta ce daya daga cikin 'yan kunar bakin wakenta ya tarwatsa motar da yake ciki mai shake da bama-bamai. A shekara ta 2015 ma dai irin wannan ziyara da 'yan Shi'a ke yi ta gamu da harin 'yan ta'adda, inda mutane13 suka mutu.