Zumunci saboda dokar 'yan aware a Kamaru
October 17, 2023A irin wannan yanayi da kasuwanni da makarantu gami da ma'aikatu ke garkame, wasu mazauna syankin Bamenda da 'yan awaren ke yi musu kulle sun yanke shawarar haduwa a wasu wurare na musamman da ba a fili ba domin rage wa kai takaici. A wani waje da ake shakatawa cikinsa da ake kira mile two a Nkem cikin Bamenda duk da kasancewar tituna duk fayau kowa na gida saboda hali na fargabar rashin tsaro, wata mashaya na budewa a ranakun Litinin din mako kawai, inda masu shiga ke zuwa debe wa juna kewa da rage kunci. Kafin ma a yarda a bai wa mutum abin da yake bukata, lallai ne sai ya nuna shaidar cewa mazuani ne shi a unguwar ko birnin saboda ba a maraba da bakuwar fuska.
Wanda ya mallaki wannan waje da ya fi son kawai a kira shi da suna Spice Boy, ya ce yana cinikin da ya kai Euro 50-70 kwatankwacin abin da ya dan haura Naira dubu 50-70 a ranakun da ake kyale mutane su dan fita yayin kuma da yake samun ninkin hakan a ranakun da aka hana fita. Baya ga mahada ta cikin unguwa da ake samu a Bamenda ga masu kwankwadar barasa, akwai ma wasu da ke haduwa ta zumunci tsakanin abokai da ba mashaya ba. Akwai kungiyar da ake kira da "ka san makwabcinka" da ke ta taimakon juna da kuma ta masu harkokin wasanni. Ranakun Litinin ne kowa ke gida karkashin dokar zamaan tilas ta 'yan awaren, kuma a ranar mazauna yankin ke zuwa taro da suka yi wa lakabi da Njangi. A gidajen tarukan na Njangi dai, akan tara kudin adashi wanda ake kwashewa tsakanin mambobi.