Ban Ki Moon a Gabas Ta Tsakiya
March 21, 2010A ranar Asabar babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya fara wannan ziyara ta yini biyu a yankunan Falasdinawa da kuma Isra´ila, yana mai cewa ɓangarorin nan huɗu dake duba batun yankin Gabas Ta Tsakiya, suna goyon bayan kokarin Falasdinawa na kafa ƙasar kansu.
Babban sakataren na MDD Ban Ki Moon wanda tun a ranar farko ta wannan ziyara ya gana da firaministan Falasɗinawa Salam Fayyad a Ramallah babban birnin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, a Lahadin nan ya kai ziyara Zirin Gaza dake ƙarƙashin ikon Hamas. Yankin kuma da Isra´ila da kuma Masar suka toshe kan iyakokinsa.
A wani lokaci in anjima da shi zai gana da manyan jami´an Isra´ila ciki har da firaminista Benjamin Netanyahu sannan. Ban wanda ya isa yankin kwana guda bayan da ɓangarorin huɗu dake shawarta batun yankin Gabas Ta Tsakiya suka yi kira ga Isra´ila da ta daina dukkan aikin gina matsugunan Yahudawa ´yan kama wuri zauna sannan ta fara ta yi ƙoƙarin cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya da Falasɗinawa kafin shekarar 2012 cewa yayi.
"Duniya gaba ɗaya ta yi tir da shirin Isra´ila na faɗaɗa matsugunan Yahudawa a gabashin birnin Ƙudus. Bari mu fito fili: dukkan aikace aikace na gina unguwanni a yankin da aka mamaye haramun ne saboda wajibi ne a daina. Ɓangarori huɗu sun sake jaddada matsayinsu."
Ban ya ganewa idonsa irin mummunan tasirin da gine-ginen matsugunan Yahudawa da Isra´ila ke ci gaba da yi a yankunan Falasɗinawa da ta mamaye ke yi a rayuwar al´umar Falasɗinu.
A cikin watan Nuwanban bara ne dai firaministan Isra´ila Benjamin Netanyahu ya yi shailar dakatar da gina matsugunan na wucin gadi tsawon watanni 10 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. To sai dai wannan dakatarwar ba ta haɗa da yankunan da Isra´ila ta ƙwace a lokacin yaƙin shekarar 1967 ba kuma ta haɗe shi da birnin Ƙudus.
Ita dai ƙasar Yahudun Isra´ila na ɗaukar dukkan yankin Birnin Ƙudus a matsayin babban birnin ta, iƙirarin da bai samu amincewar ƙasashen duniya ba. A kan haka mista Ban ya yi kira da a warware batun na Birnin Ƙudus.
"Ina kira ga dukkan sassan da abin ya shafa da su girmama juna kana su goyi da bayan zaman lafiya. Za mu iya kuma dole ne mu gano mafita daga batun na Birnin Ƙudus a matsayin babban birnin ƙasashe biyu da tsare-tsaren da za su karɓuwa ga kowa dangane da wurare masu tsarki."
Babban Sakataren na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya ce ɓangarorin nan huɗu dake shawarta batun Gabas Ta Tsakiya wato Majalisar tare da Amirka, Rasha da kuma tarayyar Turai suna goyon bayan ƙoƙarin Falasɗinawa na kafa ƙasar kansu. A ranar Juma´a ɓangarorin suka gana a birnin Mosko inda suka yi nuni da cewa mai yiwuwa nan da ´yan kwanaki masu zuwa za a fara tattaunawar bayan fage tsakanin Isra´ila da Falasɗinu. Tun fiye da shekara guda kenan ba a yi wata ganawa tsakanin sassan biyu ba.
A wannan makon ake sa ran isar wakilkin ɓangarorin wato Tony Blair da kuma manzon Amirka na musamman a Gabas Ta Tsakiya George Mitchell a yankin a wani yunƙuri na farfaɗo da shirin zaman lafiya.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi