Ban Ki Moon akan matsalolin Afirka
January 31, 2012A taron ƙolin da take gudanarwa a Addis Ababa, a yau talata, ƙungiyar tarayyar Afirka ta tsayar da shawarar ɗage zaɓen shugaban hukumar zartaswarta har ya zuwa lokacin taron ƙolin da zata gudanar a Lilongwe, fadar mulkin ƙasar Malawi, watan yuni mai zuwa sakamakon saɓanin ra'ayin dake akwai dangane da masu fafutukar neman wannan muƙami. A baya ga maganar zaɓen shugabannin ƙungiyar, daga cikin ajendar taron ƙolin da ya samu halarcin sakatare-janar na majalisar ɗinkin duniya Ban Ki Moon, har da nazarin matsalolin da a halin yanzu ke addabar yankunan Afirka.
Daga cikin ainihin matsalolin da a halin yanzu haka suke ci wa jama'a tuwo a ƙwarya dangane da nahiyar Afirka har da yadda al'amura ke ƙara taɓarɓarewa a Sudan da maganar ƙasashen da zasu ba da gudummawar soja ga rundunar kiyaye zaman lafiya ta AMISOM a Somaliya da tafiyar hawainiyar da ake samu ga matakan garambawul daga gwamnatin Somaliyar da kuma ƙin cika alƙawarin ƙasashe masu ba da taimako domin tinkarar mawuyacin halin da jama'a ke ciki a gabacin Afirka.
Dangane da ƙoƙarin da ake yi na neman bakin zaren warware rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan dai, sakatare-janar Banki Moon nuni yayi da cewar:
"Alalhaƙiƙa tun ba yau bane ba UNAMID ke gudanar da ayyukanta a ƙoƙrin tabbatar da zaman lafiya, amma muhimmin abin da ake buƙata shi ne goyan baya daga gwamnatin Sudan. Wajibi ne mu san dalilin mutuwar shugaban ƙungiyar JEM ta 'yan tawayen Darfur Khalil Ibrahim da kuma tasirin hakan akan shawarwarin zaman lafiyar. Muhimmin abu a yanzu shi ne gwamnati da 'yan tawaye su zauna kan teburin shawarwari domin shawo kan matsalolin dake akwai tare da haɗin kan majalisar ɗinkin duniya."
A can Somaliya kuwa, wadda rikicinta ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kuma har yau ake ci gaba da lalube a cikin duhu ba tare da an cimma nasara ba, duk kuwa da rundunar kiyayeb zaman lafiya da ƙungiyar tarayyar Afirka ta tura ƙasar, sakataren Majalisar ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya ƙara da bayani yana mai cewar:
"Ina maraba da szhawarar da majalisarb tsaro da zaman lafiya ta ƙungiyar tarayyar Afirka tab tsayar game da bunƙasa yawan rundunar kiyaye zaman lafiya ta AMISOM zuwa dakaru dubu goma sha bakwai da ɗari bakwai. Tuni na labarta wa kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya game da hakan kuma ina fata zai amince da shawarata kafin taronmu akan Somaliya a birnin London ran 23 ga watan fabarairu mai kamawa. A ziyarar da na kai Somaliya watan disemban da ya wuce sai da na ƙara ƙarfafa wa gwamnatin riƙon ƙwarya da ta aiwatar da taswirar zaman lafiyarv da aka zayyana wa ƙasar ta kuma yi amfani da 'yan yankunan da aka ƙwata daga dakarun Al-Shabab domin kafa hukumomin da zasu wanzar da taswirar zaman lafiyar kafin watan agusta mai zuwa. Na faɗa wa shugaba Sheikh Ahmad cewarv wajibi ne a aiwatar da wannan shiri, wanda majalisar ɗinkin duniya ta amince da ta ba shi goyan baya har ya zuwa ƙarshen watan agusta mai zuwa."
A can gabashin Afirka dai har yau mutane na cikin hali na ƙaƙa nika yi sakamakon fari da yunwar dake addabar yankin duk kuwa da taimakon da ƙasashe da kuma ƙungiyoyin agaji suka sha famar yi. Shi kansa sakatare-janar Ban Ki Moon sai da ya haƙiƙance da hakan, sannan ya ƙara da cewar:
"Har ana fama da mummunan giɓi wajen gabatar da taimakon da ake buƙata. Har yau kwalliya ba ta mayar da kuɗin sabulu game da kiraye-kirayen da muka sha famar yi ba. Kimanin mutane miliyan huɗu suka tagayyara a halin yanzu haka, a yayinda wasu dubu metan da hamsin ke fama da mummunar yunwa. Muna buƙatar ƙarin taimako, kuma zan yi amfani da wannan damar domin godo ga gaggan ƙasashen dake ba da taimako da su ƙara ƙara ƙarfafa goyan bayan da suke bayarwa bisa manufa."
Mawallafi: Getachew Tedla/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi