Ban Ki-moon ya bukaci karin soje a Bangui
February 21, 2014Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar ya tura karin dakaru a kalla dubu uku da zasu hada da sojoji da 'yan sanda ya zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin gaggawa domin sanya tsari tare da kariyar fararan hula a wannan kasa.
Ban Ki-moon ya kara da cewa wadannan dakaru za su isa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar ba da jimawa ba, kuma tare da isassun kayan aiki musamman ma jiragyen zirga-zirga a cikin wannan kasa mai Fadin gaske.
A halin yanzu dai, dakarun kasar Faransa dubu biyu, da na kasashen Afirka dubu shida, sannan da na Tarayyar Turai a kalla dari biyar ke wannan kasa. Amma duk da haka ana ganin karin dakarun na Majalissar Dinkin Duniya, wani babban abun da ake jira ne.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe