Ban Ki Moon ya goyi bayan kara yawan dakaru a Sudan ta Kudu
December 24, 2013A dangane da fadan da ake ci-gaba da yi a Sudan ta Kudu, Majalisar Dinkin Duniya za ta tura karin sojoji 5000 don rubanya yawan dakarunta a wannan kasa. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya ba wa Kwamitin Sulhu da ke birnin New York izinin daukar wannan mataki. Jakadiyar Amirka a Majalisar Samantha Power ta ce dukkan kasashe sun nuna shirin ba da goyon baya. Sai dai har yanzu ba a san kasashen da za su ba da gudunmawar sojojin ba. Da yawa daga cikin sojoji kimanin 7000 da yanzu haka ke aiki karkashin tutar Majalisar a Sudan ta Kudu, 'yan kasar Indiya ne. A dai kasar ta Sudan ta Kudu magoya bayan shugaban kasa Salva Kiir na fafatawa da masu biyayya ga tsohon mataimakinsa Riek Machar, inda rahotanni suka tabbatar da mutuwar daruruwan mutane. Sannan fararen hula dubu 45 sun nemi mafaka a sansanonin MDD. Amirka dai ta ce shugaba Kiir ya nuna shirin tattaunawa da Machar ba tare da wani sharadi ba. Wani labarin ya rawaito Majalisar Dinkin Duniya na cewa an gano gawarwaki 75 na 'yan kabilar Dinka da aka binne a cikin wani makeken rami kasar ta Sudan ta Kudu.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh