Ban Ki Moon ya kai ziyarar ba zata a birnin Bangui
April 5, 2014Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya kai wata ziyarar ba zata a birnin Bangui, na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wannan Asabar, a wani mataki na nuna aniyar ta Majalisar ta Dinkin Duniya, kan batun tura dakarunta domin su maido da doka da oda a wannan kasa da a kullu yaumin ke cikin rikici na kashe-kashe.
Ban dai yana kan hanyarsa ce ta zuwa birnin Kigali na kasar Ruwanda, inda zai halarci bukukuwan cika shekaru 20 da kisan kiyashin da aka yi a wannan kasa. Ban Ki Moon ya yada zongo ne a birnin na Bangui inda kuma yake tattaunawa da shugabar rikon kwarya Catherine Samba-Panza.
Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya na cike da fargaba ta ganin an sake samun wani kisan kiyashin shigen na Ruwanda a wannan kasa inda zai yi bayani a gaban majalisar rikon kwarya domin sake kira ga kasashen duniya da sukai dauki ga Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya.
Mawallafi: Salisou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal