1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-moon ya soki matsayin shugaban Iran

August 30, 2012

Ban Ki-moon ya halarci taron kasashen 'yan ba ruwanmu, da ke gudana a Iran.

https://p.dw.com/p/160Gp
Blockfreien Treffen in Teheran ist mit Rede von Ajatolah Khamenei eröfnet. Bild: Rasanjani, Ban Ki Moon, Mursi
Hoto: MEHR

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban ki-moon ya tunuar da Shugaban Iran kalaman da ya yi na ƙaryata kisan da aka yi wa Yahudawa da cewa ba za a amince da su, kuma Izira'ila tana da 'yancin rayuwa, kuma ya yi kira ga ƙasashen biyu da basa ga maciji da juna da su kai zuciya nesa.

Ban ya shaida wa mahalarta taron kasashen 'yan ba ruwanmu, da aka buɗe a birnin Tehran na ƙasar Iran cewa, ya yi watsi da duk wata barazana da wata ƙasa da ke cikin Majalisar ta yi wa wata, sannan ya ce kisan da aka yi wa Yahudawa tarihi ne da ba zai shafe ba.

Akwai ƙasashe 120 da ke cikin ƙungiyar ta ƙasashen 'yan ba ruwanmu, wadda ke gudanar da taro yanzu haka a ƙasar ta Iran.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu