Kira da a dauki matakan warware matsalar 'yan gudun hijira
March 30, 2016Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi kira ga kasashen duniya da su kara yawan 'yan gudun hijirar kasar Siriya da suke ba wa mafaka. Ban ya yi wannan kira ne lokacin bude babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan 'yan gudun hijira a birnin Geneva, inda ya kara da cewa ya kamata a nuna wani zumunci na kasa da kasa. Ya ce al'ummar kasar Siriya maza da mata da yara suna sa ran samun taimako daga gamaiyar kasa da kasa. Yanzu haka dai hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashe masu arziki da bisa radin kai, su ba wa 'yan Siriya kimanin dubu 480 mafaka a cikin shekaru masu zuwa. Kawo yanzu dai 'yan Siriya dubu 178 ne aka yi wa alkawarin ba su mafaka, inji Ban. Miliyoyin 'yan kasar dai ne suka tsere zuwa kasashe makwabta sakamakon yakin da ake yi a Siriyar.