Ban Ki Moon ya yi kira ga ƙasashen duniya
July 25, 2012Da ya ke yin jawabi a gaban yan majalisar dokokin na ƙasar Bosniya da ke a yankin Balkans, ƙaasar da itama ta fuskancin kisan ƙare dangi a shekara ta 1995 a Sebrenica.
Ban Ki Moon ya buƙaci ƙasashen duniyar da su haɗa kan su guri guda domin kawo ƙarshen ta'asar da gwanatin Bashar Al Assad ke aikatawa.Wanda ya ce labarin da ke fitowa daga ƙasar na ban tsoro matuƙa, kuma ƙasar ta na daf da fadawa cikin yaƙin basasa.Rahotanin da ke zuwa daga birnin Alepo na cewar dakarun gwamnatin da na ya tawaye ko wane na ƙara jibge bradan sa a birnin inda ake ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa tsakanin sasan biyu.
Yanzu haka dai wakilan na Majalisar ta Ɗinkin Duniya da ke saka ido a Siriya, su kusan ɗari ukku sun fuce daga ƙasar, bayan da yunkurin su, na dakatar da buɗe wuta ya kasa cimma nasara.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar