1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-moon ya yi tir da harin Kano

Mouhamadou Awal BalarabeNovember 29, 2014

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a hukunta wadanda suka salwantar da rayukan fiye da mutane 100 a hare-haren bama-bama da suka kaddamar a Kano.

https://p.dw.com/p/1Dwu4
Symbolbild UNO Treffen Ban Ki-moon
Hoto: Andrew Burton/Getty Images

An tabbatar da cewa mutane 120 ne suka rasa rayukansu a hare-hare kunar bakin wake da aka kaddamar a babban masallacin kano, yayin da wasu karin 270 kuma suka sami munanan raunuka. Babban sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi tir da abin da ya faru a Kano, inda ya yi kira ga hukumomin wannan kasa da su dauki matakan gano wadanda suka yi wannan aika-aika, tare da gurfanar da su gaban kuliya.

'Yan uwan wadanda suka rasa rayukansu sun yi dafifi domin ci gaba da karbar gawarwaki a asibitocin Murtala da kuma Nasarawa. Sai dai kuma hukumomin asibitocin sun yin kira ga al'umma da su kawo gudunmawar jini domin ceton rayukan wadanda suka sami raunuka.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa 'yan uwan wadanda wannan hari ya rutsa da su, yana mai lasar takobin gwamnati za ta dauki matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.