Ban Ki-moon zai ziyarci ƙasar Iran
August 22, 2012Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban ki-Moon zai hallarci taron ƙungiyar ƙasashen yan ba ruwammu da zai gudana a ƙasar Iran, wanda zai a buɗe a mako mai zuwa. Inda ya yi watsi da kiran da Amirka da Isra'ila suka yi masa na ya ƙauracewa taron tunda dai a ƙasar Iran ake yinsa. Kakakin Sakatare janar din ya shaidawa manema labarai cewa, za mu mutunta ƙasar Jamhuriyar Islama ta Iran, inda Ban ki-moon zai yi amfani da ziyar ta sa domin nuna wa mahukunta Tehran irin fatan da ƙasashen duniya ke son gani a gare su. Kamar yadda kakakin na sa ya bayyana, wasu daga batutwan da Ban ki-moon zai tattauna da mahukunta Iran, sun hada da shirin nukiliyar ƙasar da yaƙi da ta'addanci da kare yancin bil'Adama, kazalika da batun rikicin ƙasar Siriya. Don haka Ban Ki-moon zai kasance a ƙasar ta Iran na tsawon kwanki uku.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu
RTR