1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Banbancin ra'ayoyi kan nadin Seini Oumarou

October 21, 2016

A jamhuriyar Nijar, jama'a na bayyana mabanbantan ra'ayoyi dangane da nadin da shugaba Mahamadou Issoufou ya yi wa Alhaji Seini Oumarou a matsayin wakili na musamman ga shugaban kasa a karon farko a tarihin kasar.

https://p.dw.com/p/2RXII
Seini Oumarou Vorsitzender der Partei MNSD im Niger Afrika
Hoto: MNSD

A wani kudurin da ya sanya wa hannu a ranar Alhamis din da ta gabata, shugaba Mahamadou Issoufou ya bayyana nadin Seini Oumarou shugaban jam'iyar MNSD Nasara a mukamin wakilin musamman na shugaban kasa bayan kafa sabuwar majalisar ministoci da ya yi a ranar laraba.

 

Wannan ne dai karon farko da aka kirkiro mukamin wakili na musamman ga shugaban kasa wato Haut Représentant du Président de la République a Jamhuriyar Nijar. A kan haka ne ma masana harkokin siyasa da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum suka fara sharhi kan tasirin mukamin da kuma rawar da Seini Oumarou din zai taka musamman wajen shawo kan matsalolin da kasar ke fama da su wadanda suka hada da tsaro da tattalin arziki da kuma hadin kan 'yan kasa.

Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

 

Mourtala Mamouda, dan majalisa a karkashin tutar jam'iyar MNSD Nassara, kuma wani na hannun daman Seini Oumarou ya baiyana nadin da cewa abu ne da ya dace idan aka yi la’akari da mukaman da Seini Oumarou din ya rike a baya.

 

Maman Alhaji Adamou, jami'i a ofishin ministan ilimi mai zurfi, ya baiyana Seini Omarou a matsayin mutum mai hakuri da dattaku, yana mai cewa gogewarsa a kan sha’anin mulki zata bashi damar bada gagaruwar gudunmawa wajen cigaban kasa. A waje guda kuwa wasu masana na ganin cewa babu fa’ida a kirkiro wasu sabin mukammai da hukumomi, hasali ma suka ce kashe kudi ne a wannan yanayi da ake fama da matsaloli na tattalin arziki.

 

A halin yanzu dai jama’a sun sa ido domin ganin rawa ko kuma sauyi da wakilin na musamman ga shugaban kasa, Seini Oumarou zai taka ga hadin kai da kuma ci gaban kasar Nijar.