1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangarori 4 da ke neman sulhu a GTT za su kara zage dantse

Mohammad Nasiru AwalOctober 1, 2015

Masu shiga tsakanin don samun masalaha tsakanin Isra'ila da Falasdinu za su karfafa aikinsu na ganin an farfado da shirin zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/1GhQc
USA UN PK Mogherini Treffen Nahost-Quartett in New York
Jami'ar harkokin ketare ta EU, Frederica MogheriniHoto: Getty Images/AFP/D. Reuter

Jami'ar kula da harkokin ketare ta kungiyar tarayyar Turai EU, Frederica Mogherini ta ce bangarorin nan hudu da ke shiga tsakani a yankin Gabas ta Tsakiya za su karfafa kokarin neman sulhu tsakanin Isra'ila da Falasdinu. Da farko dai wakilan bangarorin da suka hada da na Majalisar Dinkin Duniya da Amirka da kungiyar EU da kuma Rasha sun gudanar da wani taro a birnin New York a gefen babban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya. A karon farko wakilan kasashen Masar da Jodan da Saudiyya da kuma na kungiyar kasashen Larabawa sun halarci taron. Mogherini ta ce halin da ake ciki yanzu a yankin na Gabas ta Tsakiya na barazana ga yunkurin samar da masalaha ta kasashe biyu makwabtan juna. A jawabin da ya yi wa taron Majalisar ta Dinkin Duniya a ranar Laraba shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya yi barazanar janyewa daga yarjeniyoyin neman zaman lafiya da Isra'ila, saboda rashin mutunta yarjeniyoyin daga bangaren Isra'ila. A wannan Alhamis Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai yi wa taron jawabi.