1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangladesh: Sheikh Hasina ta lashe zabe

January 7, 2024

Hukumar zaben Bangladesh ta ayyana Firanminista Sheikh Hasina a matsayin wadda ta lashe zaben kasar wanda hakan zai ba ta damar sake darewa kan madafun ikon kasar a karo na 5.

https://p.dw.com/p/4axGQ
Firanministar Bangladesh, Sheikh Hasina
Firanministar Bangladesh, Sheikh HasinaHoto: AFP

Hakan na zuwa ne bayan da 'yan adawa suka kaurace wa zaben. A cewar wani kwamishnan hukumar zaben kasar, jam'iyya mai mulki ta Awami League Party ta lashe fiye da kashi 50 na kujerun majalisar kasar.

Karin bayani:Ana lissafa kuri'u a zaben Bangladesh 

Jam'iyyar adawa ta Bangladesh Nationalist Party wato BNP ta tsohuwar fimanistar kasar Khaleda Zia da kawayenta duk sun ce sun tsame kansu daga zaben ne saboda suna zargin za a tafka magudi kana ana zargin gwamnatinta da cin zarafin bil Adama da kuma murkushe 'yan adawa.

'Yan siyasar sun kuma yi kiran da firaministar yanzu Sheikh Hasina da ta yi murabus, domin ta hakan ne a cewarsu ya a tsara tare da samar da zabe mai tsafta.