1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin AfDB zai ba wa Côte d'Ivoire Euro miliyan 770

Yusuf Bala Nayaya
December 16, 2016

Bashin Bankin Raya Kasashen na Afirka (AfDB) za dai a yi amfani da kudaden wajen samar da ingantattun hanyoyi na ababan hawa a birnin Abidjan cibiyar kasuwancin kasar.

https://p.dw.com/p/2UQpx
Zentrale der Afrikanischen Entwicklungsbank
Hoto: AFP/Getty Images/S. Kambou

Hukumar zartarwa ta Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ta amince da bada bashi na Euro miliyan 770 ga kasar Côte d'Ivoire, kudaden da za a yi amfani da su wajen gyara hanyoyin mota a birnin Abidjan cibiyar hada-hadar kasuwancin kasar da ma samar da gadoji kamar yadda bankin ya bayyana a ranar Juma'ar nan.

A cewar Amadou Oumarou daraktan da ke lura da harkokin da suka shafi sufuri a bankin, wannan zai taimaka wajen kawo raguwar yawaitar cinkoson ababan hawa a titunan birnin, a rage aukuwar hadura kana a samu iska tsaftatacciya a yankin.