1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankunan Turai na janyewa daga Iran

July 31, 2007

A sakamakon matsin lamba daga Amurka gaggan bankunan Turai na janyewa daga Iran

https://p.dw.com/p/Btuq
Deutsche Bank
Deutsche BankHoto: AP

Amurka ta dade tana matsin lamba har ya zuwa ranar 23 ga watan desamban bara inda kwamitin sulhu na MDD ya yanke kuduri kan kasar iran ba tare da musu ba. A karkashin wannan kuduri an yi kira ga kasashen duniya da su daina tura wa kasar Iran kayayyakin da zasu iya taimaka mata wajen habaka ma’adanin Uranium ko sarrafa makaman kare dangi. A baya ga haka za a dora hannu kan takardun ajiyar kudin Iran guda goma sha daya da kudurin ya ambace su, saboda wai suna da nasaba da shirin kasar na nukiliya.

Kasashen kungiyar Tarayyar Turai da Rasha da kuma China sai da suka yi dari-dari da lamarin da farkon fari kafin su amince da shi, a yayinda ita kuma Amurka da kamata yayi ta bayyana gamsuwarta da wannan ci gaba. Amma hakan bai faru ba domin kuwa har ya zuwa halin nan da muke ciki fadar mulki ta White House na fatan ganin an kara kuntata wa Iran da kuma tsawwala matakan takunkumin da aka kakaba mata. Sai dai kuma a maimakon ta jira har sai MDD ta tsayar da wata shawara akai Amurkan tayi gaban kanta inda take daukar matakai na matsin lamba akan gwamnatocin da kamfanoni na ketare domin su ba ta hadin kai wajen bijirewa Iran kwata-kwata, duk da cewar kudurin MDDr bai tanadi hakan ba. Bankin Jamus na Deutsche Bank na daga cikin kafofin da wannan matsin lamba ya rutsa da su baya-bayan nan. Babbar cibiyar kudin ta Jamus ta ba da sanarwar cewar zata dakatar da aikinta kuma tuntuni ta ba da wannan sanarwar ga abokan huldarta a Iran a saboda wasu dalilai na siyasa. Amma fa har yau ba wani jami’in siyasa ko na tattalin arziki da ya fito fili yayi bayani akan hakan a hukumance a game da wannan mataki, wanda ba shakka zai yi mummunan tasiri a huldodin kudi da kasuwanci tsakanin Jamus da Iran. Amma a daya bangaren gwamnatin jamus tana ci gaba da watsi da matsin lamban Amurkan dangane da lamunin da take ba wa kamfanonin kasar dake zuba Jari a Iran. Wannan lamunin ya sanya Jamus take kan gaba wajen ma’amallar tattalin arziki da Iran, inda a shekarar bara ta fitar da kaya da yawansu ya kai na Euro miliyan dubu hudu zuwa Iran. Shugabar gwamnati Angela Merkel tayi kira ga kamfanonin Jamus da su rika yin sara suna duban bakin gatarinsu a ma’amalla da Iran, amma ta ce bukatar ta Amurka game da kaurace wa kasar kwata-kwata ba mai karbuwa ba ce.