Jana'izar Helmut Schmidt
November 23, 2015Talla
A wannan Litinin din ne dai ake gudanar da jana'izar Schmidt a matakin kasa a garin Hamburg da ke zaman mahaifarsa. A jawabin girmamawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gabatar, ta bayyana cewa Jamus ta yi babban rashi na shugaba da ke da kishin al'ummarsa. Kiyasi ya nunar da cewa akalla mutane 1,800 ke halaratar jana'izar tasa, inda za a girmama shi tare da yi masa bankwana na karshe kafin a binne shi. Schmidt wanda ya rasu yana da kimanin shekaru 96 a duniya, ya kasance shugaban gwamnatin yammacin Jamus a shekarun 1970, ya taka muhimmiyar rawa wajen magance hare-haren 'yan ta'addan Red Army Faction a wancan lokaci, tare kuma da hada kai da sauran kasashen nahiyar Turai domin aza tubalin kungiyar EU.