Barakar jam'iyyun kawance mai mulki a Nijar
April 6, 2018Duk da yake kawo yanzu daukacin jam'iyyun biyu da suka soma nuna rashin gamsuwa da sabon kundin tsarin zaben da hukumar zabe ta Ceni ta yi a baya, ba su yadda akwai rarrabuwar kai a jerin kawancen jam'iyyun da ke goyon bayan shugaban kasar Mahamadou Issoufou ba. Sai dai dukkanin alamu ya tabbata cewa jam'iyyun na zaman doya da manja. Jagoran jam'iyyar PJD Hakika Alhaji Mahamane Hamissou wanda ya yi takarar shugabancin kasa a zaben 2016, ya bayyana halinda ake ciki.
"Idan har harkar zabe ta zo ba a zancen goyon bayan wani, harka ce da kowa zaman kanshi ya ke. Kowa ta shi ta fi ce shi wajen neman kuru'in 'yan kasa."
Jam'iyyar PJD Hakika ta ce ta jima tana sukar lamirin wannan sabuwar tafiya a cikin gida, amma yanzu ne lokacin bayyana abubuwanda ba su tafiya dai dai.
Shugaban jam'iyyar PJD Alhaji Mahamane Hamissou ya koka kan yadda aka yi kundin tsarin zabe ba tare da 'yan adawa ba. "A dawo bisa tsohon kundin zabe a nemi saka CENI wanda kowa ya yarda da ita, saboda gurinmu shugaban kasa ya mika mulki ga wanda Allah ya ba amma ba a yin hakan a ciki danfara. Ba gaskiya ba ne cewa ba mu son shugaban kasa."
Kawo yanzu dai bangaren na kawancen jam'iyyun na MRN ba su bayyana matsayarsu kan wannan takun saka a hukumce ba. Korafe korafen jam'iyyar PJD hakika da shugabanta yake mashawarci a fadar shugaban kasa, na zuwa ne biyo bayan wani makamancin wannan da Jam'iyyar MPN Kishin kasa ta Ibrahim Yacouba ta yi a baya-bayannan kan sukar matakin hukumar zaben da kuma kundin na tsarin zabe code electorale.