Barazanar cutar Ebola a Laberiya
October 16, 2014Ministar mai suna Angela Cassell-Bush, tace zata kasance a gefe har tsawon wadannan kwanaki kamar yadda dokokin kiwon lafiya suka bukata. Daga nata bengare babbar jami'ar kiwon lafiyar kasar ta Laberiya Bernice Dahn, da ita ma aka killace ta har na tsawon kwanaki 21 bayan rasuwar mataimakin ta sakamakon cutar ta Ebola, ta koma ga aikin ta, bayan da kwanakin suka cika kuma lafiyar ta kalau ba tare da cutar ta bayyana a gare ta ba.
Daga nashi bengare kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi kasashe membobi da su kara yawan kudadan agaji dan yakar cutar ta Ebola da a halin yanzu tayi sanadiyar mutuwar mutane kusan 4.500, inda kasashen Yamma da dama suka kudri aniyar sanya matakan bincike kan iyakokin su.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohammed Abubakar