Barazanar farfado da kotun sojoji a Chadi
June 6, 2019Rikici tsakanin manoma da makiyaya ba bakon abu ne ba a kasar ta Chadi. Wasu 'yan kasar ta Chadi na cewa mafi yawancin lokuta dai rikicin na barkewa ne a lokacin da manoma suka nemi mayar da martani a lokacin da makiyayan wadanda akasarinsu ke yi wa manyan jami'an gwamnati da na sojojin kasar kiwon shanu ke fada wa gonakin manoman. So tari a kan hukunta manomi ko yi masa duka ko kuma kashe shi baki daya. To amma a cewar Mahamat Ahmat Alhabo wani dan siyasa a kasar ta Chadi, rikicin da aka fuskanta a baya bayan nan a gabashin kasar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 30 bakon abu ne a kasar.
To domin tunkarar wannan matsala ce ta rikicin manoma da makiyaya da ke kara kamari a kasar, shugaban Chadi Idriss Deby ya yi barazanar farfado da kotun sojoji da ke da hurumin yin shari'a ga sojoji da farar hula. To sai dai tuni aniyar shugaban kasar ta Chadi ta soma fuskantar suka daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam. Dobian Assingar wakilin kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta FIDH a kasar ta Chadi ya ce babu dalilin farfado da wannan kotu a yau.
To sai dai daga nashi bangare Evariste Ngarlem Tolde malami a Jami'ar Ndjamena, a maimakon farfado da wannan kotu, kamata ya yi gwamnatin ta inganta matakan tsaro kawai a yankin gabashin kasar inda rigingimun ke faruwa.
Sai dai jam'iyya mai mulki a kasar na ganin farfado da wannan kotu ta sojoji zai zamo hannunka mai sanda ga mutanen da ke haddasa ko kuma aiwatar da wadannan kashe-kashe. Jean bernard Padare, shi ne jami'in kula da harakokin shari'a a jam'iyyar ta Shugaba Deby: "Shugaban kasa ba zai dauki matakin da ba alkhairi ba ne ga al'ummar kasa. Ni ina ganin ya yi wannan barazana ce ta lura da hadarin da wadannan rigingimu ka iya jefa kasarmu."
A shekara ta 1990 ne bayan hawan mulkin Shugaba Idriss Deby aka kafa wannan kotu ta sojoji wacce ta zartar da hukuncin kisa da ma zartar da shi kan mutane da dama. Amma a bisa matsin lambar kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, babban taron muhawar na kasa ya soke kotun a shekara ta 1993.