1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na fuskantar barazanar takunkumi

Lateefa Mustapha Ja'afarMay 27, 2016

Kasashe bakwai da ke da karfin tattalin arziki a duniya wato G7, sun yi barazanar sake kakabawa kasar Rasha takunkumin karya tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/1IvPV
Taron G7 a Japan
Taron G7 a JapanHoto: Reuters/J. Watson

Kasashen sun ce in har Rasha ba ta shiga cikin sabon shirin kawo karshen rikicin da ake ciki a yankin Gabashin Ukraine ba to kuwa za ta fuskanci karin matsin lamba daga gare su. A wata sanarwa da shugabannin kasashen bakwai da suka hadar da Amirka da Kanada da Jamus da Birtaniya da Faransa da Italiya da kuma Japan suka fitar yayin taron tattalin arzikin da suke gudanarwa a birnin Ise-Shima na Japan, kasashen sun ce za su sake kakabawa Rashan takunkumin karya tattalin arzikin ne in har ba ta mayar da hankali wajen yin amfani da tanade-tanaden yarjejeniyar kawo karshen rikicin Ukraine da aka cimma a birnin Minsk ba. Kasashen sun kuma amince da bayar da gudunmawar sama da Euro biliyan uku domin sake gina Iraki, kana sun sha alwashin bin hanyoyin da suka kamata a siyasance domin bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya.