Coronavirus: Barazanar yunwa a duniya
April 9, 2020Ba agajin jinkai kadai ba, an ma samu nasarrorin bunkasar tattalin arziki da na siyasa a kasashe masu yawa da suka shiga wannan matsala. Misali hanyar samar da abinci ya janyo an samu matsala a wasu yankunan saboda akwai tsare-tsare, inda kananan kasuwanni suka hade da na kasa gami da kasashen duniya, abin da ya janyo samar da abinci tsakanin kasashen duniya. Wannan ya tabbatar da duniya a matsayin bai daya.
Fargabar komawa gidan jiya
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, ta yi gargadin shiga matsala sakamakon annobar cutar numfashi ta Coronavirus da ake kira Covid-19. Wannan ya faru sakamakon kusan rufe kasashe da dokokin hana fita da aka sanya, saboda wannan annoba kamar yadda Simone Pott mai magana da yawun kungiyar yaki da yunwa ta duniya ta bayyana.
A cikin kasashe ake samar da abinci da ke bin matakai domin kai wa sauran mutane a sauran sassa, sai dai hukumar samar da abinici ta Majalisar Dinkin Duniyar ta ce yanayin na cikin rudani saboda cutar Coronavirus. Hukumar ta ce a yanzu ba za ta iya gudanar da tarurruka na samar da kudi ba, kamar yadda Larissa Probst daraktar gudanarwa a wata kungiyar Jamus mai aikin tara kudin tallafi ga kungiyoyin ke cewa: "Samun taimako wajen shiryi wani biki da jawabi, duk wannan damar babu."
Ayyukan kungiyoyin agaji sun tabu
Su kansu kungiyoyin jin kai suna sake tunani saboda halin da ake ciki ya shafi aikinsu kai tsaye na matsakaici da dogon lokaci, kamar bunkasa samar da abinci mai gina jiki da horas da manoma hanyoyin inganta lafiya da ke zama mai muhimmancin a wannan lokaci, kamar yadda Simone Pott mai magana da yawun kungiyar yaki da yunwa ta yi karin haske:
Kasashe kamar Jamus na taimakon miliyoyin mutane da abinci kafin lokacin daina aiki da shi da aka tanada saboda kauce wa zubarwa. Sai dai a kasashe masu tasowa da wadanda suka fara kosawa hakan bai wadatar ba. A kasashen Indiya da Brazil annobar cutar Coronavirus ta janyo masu karanmin karfi na rasa abinci mai arha. Simone Pott mai magana da yawun kungiyar yaki da yunwa ta duniya ta yi karin haske tana mai cewa: "Wannan kai tsaye ya shafi yanayin samun abincin iyalai lokacin da dabu kudin shiga."
Mutane da yawa masu kananan ayyuka sun rasa saboda annobar ta Coronavirus, inda ake kara shiga mawuyacin hali.