Senegal na cikin halin tsaka mai wuya
June 7, 2023Yanayin jin dadin da kasar Senegal ta samu a baya wadda dimukuradiyyarta ta kasance abar misali a nahiyar Afirka, lamarin a yanzu yana nema ya gagari kundila
Akalla mutane 16 ne suka mutu, wasu daruruwa kuma suka jikkata yayin da masu zanga-zanga suka yi arangama da jami'an tsaro, wanda ya zama tarzoma mafi muni da aka taba fuskanta cikin shekaru da dama a kasar da ke yammacin Afirka.
A yayin tarzomar dai an yi ta kwasar ganima a gine-gine masu zaman kansu da ma na daidaikun jama'a gami da wuraren kasuwanci, wadanda suka hada da gine-ginen jami'o'i da gidajen mai da bankuna da manyan kantuna, har ma da tashoshin mota. Gwamnati da 'yan adawa a Senegal dai na zargin juna da hannu a hasarar rayukan da aka samu.
Masana na gargadin cewa tattalin arzikin kasar zai fada cikin matsanancin hali bayan zanga-zangar da ta yi sanadiyar rayuka. Tashe-tashen hankula na kwanaki biyu sun janyo hasarar biliyoyin CFA, dubun dubatan daloli a daya hannun, da kuma yadda hadarin siyasa ke yin barazana ga ci gaban da ake samu a wannan shekarar.
Sai dai kuma, a wata hira da ya yi da DW, wani dan jarida kuma mai sharhi kan al'amuran zamantakewa Adolphus Mawolo ya ce duk da cewa fadan da aka yi a Senegal ya nuna kasar da mummunan matsayi, ba zai zame koma baya na tattalin arziki ba.
"Ya ce gwamnati za ta nuna cikakken karfin iko kan lamarin, ban ga wani dan adawa ko wani a cikin kungiyoyin farar hula da zai sake sa mutane su fita kan tituna ba."
Senegal dai ta dade da yin kaurin suna wajen samun kwanciyar hankali a yankin Afirka da ke fama da juyin mulki. A cikin kasar da ke da fama da karancin kariya a harkar zamantakewa, yawancin al'umma suna rayuwa cikin damuwa da barci da ido daya.
Magaye Gaye mai shekara 19 da ke da shagon sayar da kayayyakin masarufi a kasuwar Sandaga da ke birnin Dakar, ya ce tun a jajibirin zartar da hukuncin ya rufe rumfarsa. Ya ce lamarin ba mai sauki ba ne na zama a gida tsawon kwanaki ba tare da bude shago ba, saboda ya kashe kusan komai da ke hannunsa.
Tun bayan barkewar rikicin a makon da ya gabata, wasu malaman addini suka yi kira da a kwantar da hankula. Bayan ziyartarsa da shugaba Macky Sall ya yi a karshen mako, fitaccen malamin addinin Islama Serigne Bassirou Mountakha Mbacke, ya yi kira ga jama'ar birnin Touba, hedikwatar darikar da yake jagoranta, da su daina zanga-zangar su koma gida.
Kamar sauran abokan hamayyar Shugaba Sall da suka gabata, magoya bayan madugun adawa Ousmane Sonko sun yi zargi magudi da cin zarafi a tsarin shari’ar kasar, zargin da shugaban kasar ya musanta. Sai dai Sall ya zuwa yanzu, ya ki fitowa fili ya bayyana karara ko zai tsaya takarar shugabancin kasar a karo na uku, matakin da masu suka ke ganin zai saba wa kundin tsarin mulkin kasar.