1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barcelona da PSG na tattauna cinikin Neymar

Gazali Abdou Tasawa
August 13, 2019

Wata tawagar shugabannin kungiyar Barcelona ta isa a wannan Talata a kasar Faransa domin tattaunawa da shugabannin kungiyar PSG kan batun cinikin shahararren dan wasan nan na kasar Brazil wato Neyma.

https://p.dw.com/p/3NqLr
Fußball WM 2018 Brasilien vs Mexiko Torjubel
Hoto: Reuters/C.G. Rawlins

Wata tawagar shugabannin kungiyar Barcelona ta isa a wannan Talata a kasar Faransa domin tattaunawa da shugabannin kungiyar PSG kan batun cinikin shahararren dan wasan nan na kasar Brazil wato Neyma da ke son ficewa daga kungiyar tasa ta PSG ko ta halin kaka, domin komawa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona. 

Zuwan tawagar jami'an kungiyar ta Barcelona da suka hada da daraktan kula da harakokin wasanni Eric Abidal dan asalin kasar ta Faransa ta isa birnin Paris a matsayin wani babban ci gaba a batun cinikin dan wasan ta la'akari da yadda a baya kungiyar ta PSG ta ki amincewa da tattaunawa kai tsaye da wakillan kungiyar ta Barcelona. Barcelona ba ta da kudi tsaba na aiwatar da wanann ciniki, dan haka take son hadawa da 'yan wasa kamar Philippe Coutinho ko Ivan rakitic a cikin cinikin dan wasan da ke zama mafi tsada a duniya. 

Sai dai PSG ta bayyana cewa tana bukatar kudi ne tsaba a cinikin dan wasan wanda ta saya sama da miliya 222 na Euro. Wannan ce ta sanya wasu masu sharhi kan harkokin wasannin kwallon kafa a kasar ta Faransa ke ganin zuwa wakillan kungiyar ta Barcelona a Paris a wannan Talata ba ya nufin cewa kungiyoyin biyu za su cimma matsaya kan batun cinikin dan wasan wanda dama babbar kishiyar kungiyar ta Barcelona wato Real Madrid ke son saya ita ma.